Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ganawar da Mahmud Abbas ya yi da ministan yaki na Isra’ila yana zuwa ne adaidai lokacin sojojin Isra’ila suke ci gaba da farma masu zanga-zangar ci gaba da gine gine matsugunnan yahudawa a yankunan falasdinawa da ta mamaye a gabar yammacin kogin Jodan dama wasu sassa daban daban.
Mahamud Abbas ya ziyarci gidan wani babban jami’in Isra’ila a karon farko a cikin shekara 10, kuma bangarorin biyu sun tattaunawa kan muhimman batutuwa da suka shafi tsaro a ganawar tasu ta tsawon sao’I 2.5 , kuma wannan itace ganawa ta 2 da bangarori suka yi tun bayan kafa sabuwar gwamnatin Isra’ila.
342/